Ko ka tsaya A Daura ko ka tafi Nijar za mu neme ka”: Tinubu Ga Buhari
Zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, ya fada ma shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa za a dunga neman gudunmawarsa a duk inda yake bayan barin mulki
Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da yake martani ga furucin da shugaban kasar ya yi cewa watakila Nijar zai koma da zama bayan barin mulki a ranar 29 ga watan Mayu
Da yake jawabi bayan karrama shi da lambar yabo ta kasa, Tinubu ya fada ma Buhari cewa ya sa ran jin sallama a kofarsa, imma a Daura, Nijar koma a duk inda yake
Zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, ya fada ma shugaban kasa Muhammadu cewa za su neme shi a duk inda zai gudu ya je bayan barin kujerar mulki a ranar 29 ga watan Mayu.
Da yake martani ga furucin da shugaban kasar ya yi a ranar Talata, 23 ga watan Mayu cewa Nijar za ta cece shi idan wani ya biyo shi bayan ya bar mulki a ranar Litinin, Tinubu ya bayyana cewa a duk inda shugaban kasar zai koma bayan mulkinsa, ya sa ran amsa kira.
Zababben shugaban kasar ya yi furucin ne yayin da yake jawabi bayan karrama shi da lambar yabo ta GCFR tare da zababben mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, wanda aka karrama da GCON.
Tinubu ya kuma bayyana cewa yana sane da tarin kalubalen da ke gabansa da zaran ya karbi mulki a ranar 29 ga watan Mayu. Ya kuma godema shugaban kasar kan karrama shi da mataimakinsa da lambar yabo ta kasa.
Ya ce kuma yi iya yinka, ya mai girma shugaban kasa. Yanzu, babban aiki zai hau kaina. Na san ma’anar lambar yabon da aka bani a yau da kuma girman aikin da ke jirana. Ko ka tafi Daura, Nijar, ko ko’ina, ka sa ran jin sallama a bakin kofarka.”
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim