Ko-odinetan Kwankwaso ya fice daga NNPP zuwa PDP a Bauchi.
Kodinetan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar (NNPP) na jihar Bauchi, Dr Babayo Liman, ya fice daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar PDP.
Babayo Liman, kuma shi ne Sakataren Jam’iyyar na shiyyar Arewa-maso-Gabas, ya sanar da murabus dinsa a wani taron manema labarai a ranar Litinin a Bauchi.
A cewar sa; “Ina so in sanar da jama’a musamman ‘yan jam’iyyar NNPP na jihar Bauchi da Arewa maso Gabas da Najeriya baki daya cewa na yi murabus daga matsayina na dan jam’iyyar NNPP.
Na kuma yi murabus daga matsayina na Sakatare na shiyyar Arewa maso Gabas da kuma mamba kuma kodineta na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na dan takarar shugaban kasa na NNPP, Dr Kwankwaso.
“Bari jama’a su sani cewa na janye daga jam’iyyar NNPP, ba ni ba jam’iyyar NNPP daga yau,” inji shi.
Ya ce ya fice daga NNPP zuwa PDP tare da dimbin magoya bayansa, inda ya ce jam’iyyar ba ta da tsarin da za ta iya lashe zabe a kasar nan.
Ya ce ya yanke shawarar sauya sheka ne hakan ya samo asali ne daga rikicin cikin gida da rashin bin doka da oda da rashin hadin kai a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar saboda rashin shugabancin jam’iyyar.
A cewarsa, shugabancin jam’iyyar NNPP ba ta gudanar da al’amuranta da kyau wanda ya haifar da bullar bangarori daban-daban.
Ya zayyana kuri’u ga jam’iyyar PDP da ‘yan takararta a dukkan matakai a zabe mai zuwa.