Kotu a Kano ta umarci wani mutum da ya yanka zakararsa wanda ya Addabi makwabta
Kotu a Kano ta umurci wani mutum da ya yanka Zakararsa aboda yana takurawa makwabtaka.
Wata Kotun Majistare da ke Gidan Murtala a Jihar Kano, ta umurci Isyaku Shu’aibu, mamallakin wani zakara da ya shahara da kururuwa, da ya yanka shi saboda tada hankalin makwabta da kuma hana su barci.
Wani makwabcin wanda ake kira mai suna Yusuf Muahmmad Ja’en ne ya shigar da kara a gaban kotun inda ya ce kukan zakara ya dagula musu barci da kwanciyar hankali a unguwar, kamar yadda Aminiya ta ruwaito a ranar Alhamis.
Mai zakaran, ya tabbatar da cewa ya yi cara sosai, amma yana shirin yanka shi nan ba da dadewa ba.
Alkali mai shari’a Halima Wali wadda ta jagoranci shari’ar ta umarci Shu’aibu da ya yanka zakara da zarar ya fito daga kotun.
Maigidan ya roki kotun da ta kara masa wa’adin hutu kafin lokacin yanka Zakarar zuwa juma’a.
Alkalin kotun, wanda ya gamsu da hujjar masu korafin, ya amince kuma ya yanke hukuncin cewa za’a a yanka Zakarar a ranar 7 ga Afrilu, kasancewar Barka da Juma’a.