Kotu ta daure Wani dan kasuwa sakamakon kamashi da laifin damfarar mai sayar da Tumatur a Jos.
An Daure Dan kasuwa wata shida a gidan yari bisa samunsa da laifin damfarar mai sayar da tumatur.
Wata Kotun Majistare da ke Jos a ranar Juma’a ta yanke wa wani dan kasuwa, Abubakar Usman, mai shekaru 28, hukuncin daurin watanni shida a gidan yari bisa samunsa da laifin damfarar wani mai sayar da tumatur.
Majistare Shawomi Bokkos ta yankewa Usman hukuncin ne bayan ya amsa laifuka biyu da suka hada da karya amana da zamba.
Bokkos ya ce hukuncin zai zama hana wasu da ke son aikata irin wannan abu.
Alkalin kotun ya baiwa mai laifin zabin biyan tarar N10,000.
Ya kuma umurci mai laifin da ya biya diyyar N50,000 ga wanda ya kai kara.
Tun da farko, Lauyan masu gabatar da kara, Insp Ibrahim Gokwat, ya shaida wa kotun cewa an kai karar ne a ranar 4 ga watan Mayu, a ofishin ‘yan sanda na Laranto ta hannun Ms Anagor Ugo, mai shigar da kara.
Gokwat ya ce an bai wa wanda aka yankewa hukuncin Naira 50,000 don ya ba da kwanduna 20 na Tumatir, kuma ya mayar da kudin zuwa amfanin kansa.
Dokar, ya ce hukuncinsa ne a karkashin dokar Penal Code na Filato.
Rahoto: Kamal Aliyu Sabongida