Kotu Ta Fara Tuhumar Wani Matashi Sakama Kamasa Da Laifin Sace Laifukan Màsàllaci A Kano.
An Gurfanar Da Wani Matashi A Gaban Kotun Shari’ar Musulunci Bisa Zargin Sace Lasifikar Masallaci A Kano.
An gurfanar da wani matashi mai shekara 20 a gaban kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a birnin Kano, bisa zargin aikata laifin satar lasifikar masallaci.
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa matashin mai suna Halifa Sani, wanda ya ke a Gadon Kaya cikin birnin Kano, an gurfanar da shi a gaban kotun ne ranar Laraba, 7 ga watan Yunin 2023.
A na zargin matashin ne dai da shiga cikin masallacin Usman Ibn-Affan da sace sifikar masallacin da kuma wayar kebur waɗanda kuɗinsu sun kai N70,000.
Rahoton wannan aika-aikar da matashin ya aikata ne a ofishin ƴan sanda a ranar 2 ga watan Yunin 2023.
Mai shigar da kara, jami’in dan sanda mai matsayin sufeta, Abdullahi Wada, ya bayyana cewa wani Malam Nura Mohammed shine ya kai korafin satar da matashin ya yi a gaban yan sanda.
Abdullahi ya bayyana cewa Malam Nura ya shigar da korafin ne a ofishin yan sanda na Gwale cikin birnin Kano a ranar 2 ga watan Yunin 2023.
Mai shigar da karar ya bayyana cewa wanda ake karar ya sace lasifika ta masallacin Usman Ibn-Affan wacce kudinta sun kai N50,000 da wayar kebur wacce kudinta sun kai N20,000.
Sai dai wanda ake karar bisa zargin tafka sata a masallaci ya musanta aikata laifin da ake tuhumarsa da shi a gaban kotun.
Alkalin kotun, mai shari’a Malam Umar Lawal-Abubakar, ya bayar da belinsa kan kuɗi N10,000 da sharadin dole sai wani mutum daya ya tsaya masa wanda ya ke dan’uwansa na jini.
Alkalin ya kuma dage sauraron karar har sai zuwa ranar 22 ga watan Yuni domin ci gaba da shari’ar.
Rahoto Hassana Magaji