Daga Rafi’atu Mustapha Katsina.
Wata babbar kotun jihar Ribas da ke zamanta a birnin Fatakwat ta tsare wasu mutum hudu a gidan yari saboda zargin fashi da makami a gidan matar tsohon shugaban Najeriya Patience Jonathan.
Ana tuhumar matasan da laifuka biyar da Suka hada da hadin baki, da sata, da fashi da makami, da kuma yunkurin kisan kai.
Ana dai zargin mutanen hudu da kutsawa gidan matar tsohon shugaban kasar wanda ke unguwar G.R.A a birnin Fatakwat inda suka saci kayayyaki na miliyoyin nairori.
Zargin da matasan hudu duka suka musanta bayan karonto musu tuhumar a gaban kotu.