Kotu ta tura wani dattijo zuwa gidan yari saboda laifin bata kudi kwandaloli.
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta gurfanar da wani dattijo kan laifin bata kudin kasa
Jami’an hukumar NDLEA ne suka fara kama mutumin wanda a yayin gudanar da bincike ne suka gano tsabar kudade a tattare da shi
Mutumin ya bayyana cewa sama da shekaru 25 kenan da yake wannan sana’a ta sarrafa tsabar kudade zuwa kayan ado
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arziƙin kasa zagon kasa (EFCC) reshen jihar Kaduna, ta gurfanar da wani dattijo a gaban kotu.
EFCC ta dai gudanar da mutumin mai suna Ibrahim Musa Dabai a gaban mai shari’a M.N Yunusa na babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano.
EFCC ta tuhumi mutumin ne da laifin tozartar da kudaden Najeriya, kamar yadda Daily Nigerian ta wallafa.
Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta ƙasa (NDLEA) suka fara kama Mista Ibrahim a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
A yayin gudanar da bincike ne suka same shi tare da tsabar kuɗi da ya yi ikirarin cewa yana amfani da su ne wajen yin kayan ado domin siyarwa.
Bayan hakan ne, hukumar ta NDLEA suka mika shi zuwa hannun hukumar EFCC domin ci-gaba da bincike.
A yayin gudanar da bincike, mutumin da aka yankewa hukuncin ya bayyana cewa ya shafe shekaru 25 yana sana’ar canza tsabar kudi zuwa kayan ado da suka hada da zobe, ‘yan kunne, mundaye da sauransu.
“Kai Ibrahim Musa Dabai wani lokaci a cikin watan Maris, 2023 a Kano, a karkashin ikon babbar kotun tarayya, bisa rajin kanka, ka yi ta’ammali da kudin Najeriya : tsabar kuɗi da babban bankin Najeriya (CBN) ya samar, a lokacin da ka yi amfani da su domin kera kayan ado domin yin kasuwanci, don haka ka aikata laifi da ya sabawa sashe na 21 (1) na dokar babban bankin Najeriya ta 2007”.
Lauyan masu shigar da kara, N. Salele ya bukaci kotun da ta hukunta wanda ake tuhuma bisa laifin da ya aikata.
Mai shari’a Yunusa, ya yankewa mai laifin hukuncin daurin watanni 3 a gidan yari ko kuma tarar Naira 30,000.
Bugu da kari, za a mayar da kudaden da ya riga ya sarrafa zuwa ga babban bankin Najeriya (CBN), domin a lalata su kamar yadda dokar CBN ta 2007 ta tanada.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim