Kotu ta wanke dan gwamnan Bauchi bisa zarginsa da al’mundahana na biliyan 1.1.
Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ta sallami Shamsudeen Bala, dan Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed wanda ake tuhuma da laifin almundahana kimanin Naira biliyan 1.1 tare da wanke shi.
A wani hukunci da ya yanke a ranar Talata, Mai shari’a Nnamdi Dimgba ya ce masu gabatar da kara sun gaza tabbatar da zargin da ake yi musu ba tare da wata shakka ba kamar yadda ake bukata a karkashin dokar.
Mai shari’a Dimgba ya na da ra’ayin cewa masu gabatar da kara sun gaza yin cikakken bayani da kuma karyata ikirarin wanda ake kara na cewa yana cikin rudani yayin da yake bayyana kalamansa ga masu binciken EFCC.
Alkalin ya lura cewa asusun bankin wanda ake kara, wanda ya kasa bayyanawa a cikin fom din bayyana kadarorinsa, matarsa ce ke sarrafa shi, bayan aurensu.
Ya ce: “Asusun da aka fada ba ya karkashin ikonsa (Bala) amma a karkashin matarsa.
“Masu gabatar da kara za su iya yin bincike sosai kan ikirarin wanda ake kara na cewa ya aikata cikin tashin hankali da rudani lokacin da yake cike fom din bayyana kadarorin.
“Masu gabatar da kara ne kawai ke da ikon ruguzawa da kuma binciken kimiyance kan ikirarin wanda ake kara dangane da halin da yake ciki a lokacin kama shi,” in ji alkalin.
Mai shari’a Dimgba, a wani hukunci da ya yanke kan rashin gabatar da karar Bala, ya yi watsi da tuhume-tuhume 11 cikin 20 da ake tuhumar sa da aikatawa.
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ce ta gurfanar da Bala tare da wasu kamfanoni hudu – Bird Trust Agro Allied Ltd, Intertrans Global Logistics Ltd, Diakin Telecommunications Ltd da Bal-Vac Mining Ltd.
Hukumar EFCC ta yi ikirarin cewa, kamfanonin Bala ne ya yi amfani da su wajen karkatar da sama da N1.1b.
An yi zargin cewa Bala ya ci gaba da samun gidaje a cikin manyan lungunan Abuja da ya biya kudi, domin boye kudaden da ya sata a hannun sa.
Hukumar ta kuma yi ikirarin cewa wasu daga cikin kadarorin sun hada da filaye guda biyar a gonar Asokoro; House FS 2 B, Green Acre Estate Apo-Dutse, Abuja; House FS 1A, Green Acre Estate, Apo-Dutse; FS 1B, Green Acre Estate, Apo-Dutse, Abuja and House 2A, No. 7, Gana Street, Maitama, Abuja.
Rahoto: Kamal Aliyu Sabongida