Kotun Shari’ar Muslunci Ta Bayar Da Umarnin A Chafko Mata Sheikh Abdul’aziz Idiris
Wata kotun shari’ar musulunci ta bayar da umarni ga jami’an tsaro da su kamo mata sanannen malamin addinin musulunci a Bauchi
Kotun ta bayar da umarnin ne bayan Sheikh Abdul’aziz Dutsen Tanshi ya ki halartar zaman ci gaba da shari’ar da ake masa
Lauyoyin wanda ake karar sun gayawa kotun cewa baya da lafiya ne, uzurin da kotun ba ta gamsu da shi ba kwata-kwata
Kotun shari’ar musulunci mai zamanta a jihar Bauchi, ta ba jami’an tsaro umarnin su cafko mata Sheikh Abdul’aziz Idris Dutsen Tanshi.
Kotun ta bayar da umarnin ne saboda malamin ya ki halartar zamanta na ranar Laraba, 31 ga watan Mayun 2023, rahoton Aminiya ya tabbatar.
Umarnin kotun ya zo ne a yayin ci gaba da zaman sauraron shari’ar malamin wanda aka gurfanar bisa zargin yin batanci ga manzon Allah (SAW), da kuma tada zaune tsaye. Sheikh Abdul’aziz ya musanta zarge-zargen da ake yi masa.
Bayan an tsare malamin addinin musuluncin a gidan gyaran hali, ya samu beli a ranar 22 ga watan Mayu, bayan ya cika sharuddan da kotun ta gindaya masa, a zaman da ta yi na karshe kan shari’ar.
Bayan kotun ta bayar da belinsa ta kuma dage ci gaba da sauraron shari’ar har zuwa ranar 31 ga watan Mayun 2023, cewar rahoton Tribune.
Sai dai a yayin da kotun ta ci gaba da zamanta na jiya Laraba, malamin addinin musuluncin bai samu halartar zaman kotun ba.
Lauyoyin wanda ake karar sun gayawa kotun cewa malamin ya kasa halartar zaman kotun ne saboda yana fama da rashin lafiya.
Sai dai kotun ta sa kafa ta yi fatali da uzurin da lauyoyin wanda ake karar suka kawo, inda ta ce hakan raina darajar kotu ne.
A dalilin hakan sai kotun ta bayar da umarni ga jami’an tsaro da su cafko mata shi domin ci gaba da fuskantar shari’a.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim