Ku Daina Sanya Tufafi Kamar Mata a yayin gangami, Binani ta gaya wa maza magoya bayanta.
Yar takarar gwamna a jam’iyyar APC a jihar Adamawa, Sanata Aishatu Ahmed Binani ta yi kira ga magoya bayanta da su yi suturar jinsin su kamar yadda Allah ya yarda.
Ta kuma nemi mazan da ke sanye da kayan mata zuwa gangamin yakin neman zabenta ko duk wani abu makamancin haka da su daina.
Punch ta ruwaito cewa wasu matasa maza ne ke ci gaba da goyon bayan Binani har suka kai ga sanya tufafin mata domin nuna farin cikinsu da cewa Binani shi ne dan takarar gwamna a jam’iyyar APC.
Binani, ya fusata ne a wajen wani gangamin yakin neman zabe da aka gudanar a garin Gombi da ke karamar hukumar Gombi a jihar a karshen mako.
Yayin da ta ke gode wa mutanen da suka ba ta goyon baya, ta yi kira ga wadanda suke sanye da tufafin mata da su daina, domin tana mutunta dukkan maza kuma tana fatan maza su kasance maza.
Ta roki al’ummar Gombi da su kada kuri’a ba ita kadai ba a lokacin babban zaben da za a yi, amma duk ‘yan takarar APC daga sama har kasa.
Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Gombi/Hong Yusuf Kyaftin Buba ya shaidawa al’ummar Gombi cewa zaben Binani da daukacin ‘yan takarar jam’iyyar APC zai kara karfafa nasarorin da aka samu kawo yanzu.
Ita ma wata fitacciyar mai goyon bayan Binani, Ambasada Fati Balla ta ce yanzu lokaci ya yi da za a bai wa mace kyakkyawar dama ta shugabanci jihar Adamawa ta kuma zama zababben gwamna mace ta farko a Najeriya.
Ta ce Binani ta kware musamman a ofis bayan yadda ta taka rawar gani a ma’aikatun siyasa da farko a matsayinta na ‘yar majalisar wakilai da kuma Sanata.
Rahoto: Kamal Aliyu Sabongida.