“IGP na ƙasa ya nuna alhininsa kan yadda Ƴan Najeriya ke yiwa Ƴan sanda mummunar zato, Dan Allah a daina yi wa ƴan sanda mummunar fahimta, IGP na ƙasa baki ɗaya ya roƙi ƴan Nijeriya.
“Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, IGP Usman Alkali-Baba, ya buƙaci Ƴan Najeriya da su sauya fahimtar su kan Ƴan sanda, domin inganta ayyukansu.”
“Alƙali-Baba, wanda kwamishinan Ƴan sanda Ade Hamzat ya wakilta, ya bayyana hakan ne a jiya Laraba a wani babban taron Ƴan sanda na yini ɗaya mai taken: “Sabbin Manufofin Aikin Ɗan Sanda a Nijeriya.”
“Ofishin gyaran fuska da Cigaban na Ƴan sanda, PORTO ne ya shirya taron tare da goyon bayan sauran abokan hulda da suka hada da Cleen Foundation da “MacArthur Foundation”
“IGP din ya ce akwai buƙatar a sauya mummunar fahimta da jama’a ke yi wajen yin mu’amala ga ‘yan sanda a yayin gudanar da ayyukansu.
“Dole ne a samu ingantaccen sauyi na ra’ayin jama’a game da Ƴan sanda domin a samu daidaiton sauye-sauyen aikin ‘yan sanda a kasar,” in ji shi.
“Kamar yadda na faɗa, su ma ‘yan sanda a na cin zarafinsu, Lokacin da muka yi aikin ɗan sanda a da abokan aikin mu a wajen Najeriya kuma mu ka ga hadin kan da ‘yan sanda ke samu da ga jama’a, kuma muka kwatanta ayyukanmu a wajen Najeriya, sai mu ka gano cewa bambamcin aikin ɗan sanda a can da nan gida Nijeriya a bayyane ya ke.
“Saboda a Najeriya, ƙungiyoyin farar hula na goyon bayan jama’a, amma su wane ne suke goyon bayan Ƴan sanda saboda an tauye haƙƙinsu su ,” in ji shi
“IGP ya ƙara da cewa Ƴan sanda abokan al’umma ne, bihasalima abokan zaman lafiya da kowa a ƙasar nan, abin nufi yana kira ga Ƴan Najeriya da su riƙa bawa Ƴan sanda haɗin kai domin tabbatar da zaman lafiya a Najeriya.”
Labari: Rufa’i Abdulrazak Bello Rogo.