Halifancin Abbasiyawa ita ce halifanci na uku da ya gaji Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam, Daular da ta fito daga zuriyar kawun annabi Abbas bn Abdul-Muddalib ce ta kafa ta.
Me Aka San Khalifancin Abbasiyawa Da Shi?
Khalifofin Abbasiyawa ne suka kafa birnin Bagadaza a shekara ta 762 miladiyya. Ta zama cibiyar ilmantarwa kuma cibiyar abin da ake kira shekarar Zinare na Musulunci.
Wane Ne Ya Yi Nasara A Kan Halifancin Abbasiyawa?
Mamayewar Mongol.
Abbasiyya khalifa. Halifancin Abbasid, na biyu daga cikin manyan dauloli biyu na daular musulmi ta halifanci, sun yi sarauta a matsayin khalifancin Abbasiyawa har zuwa lokacin da mamayar Mongol ta kifar Da Daular a shekara ta Dubu Ɗaya da Ɗari Biyu da Hamsin da Takwas (1258).
Abbasiyawa sun sami sunan su ne daga zuriyar Abbas bn Abdul Muɗɗalib. Abbas kawun Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam ne kuma ɗaya daga cikin sahabbansa.
Abbasiyawa sun ɗaga tutar fatattakar umayyawa daga kan shugabantar musulunci wato (Khalifa) don ƙwatarwa wa Ahlul Baiti hakkinsu wato ƙwatar musu gadon halifanci.
Abbasiyawa sun hamɓarar da daular Umayyawa a shekara ta 750 Miladiyya, tare da goyon bayan mawali, ko kuma waɗanda ba larabawa ba, ta hanyar mayar da babban birnin daular tasu zuwa Bagadaza a shekara ta 762 Miladiyya.
Daular Abbasiyawa ta fara kafa gwamnatinta ne a Kufa, Iraƙi ta zamanin nan, amma a shekara ta 762 halifa Al-Mansur ya kafa birnin Bagadaza, kusa da tsohon babban birnin na Babila. Farkon mulkin Abbasiyawa lokaci ne na zaman lafiya da wadata.
An sami babban ci gaba a fannoni da yawa na kimiyya, lissafi, da likitanci. An gina makarantu ƙananu da manyan makarantu da ɗakunan karatu a ko’ina cikin daular. Al’adar ta bunƙasa yayin da fasahar Larabci da gine-gine suka kai ƙololuwar ɗaukaka.
Yawancin lokaci ana kiransa da Shekarun zinare na Musulunci.
Shekarar 909 daular Abbasiyawa ta samu wawakeken giɓi bayan ɓallewar ƴan tawayen Shi’a na Isma’iliy wanda suka kafa daular Faɗimiyya (fadimist)
Sun Zargi daular ne ta Abbasiyawa su ma da hana ƴan asalin iyalan Nana Faɗima (RA) jagoranci inda shugabansu, Abdullah al-Mahdi Billah ya ayyana kansa a matsayin jinin faɗima ƴar manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.
Sun zargi daular abbasiyawa da bin mazahabi na sunnah sannan da bin tsarin siyasa hakan ya sa suka yi bore suka kafa tasu daular ta Faɗimiyya, ma’ana, iyalan Nana Faɗima (AS).
Sun gangaro zuwa Misra (Misira) inda suka kafa su ma tasu daular, a nan a hankali suka samu goyon bayan sosai a Afrika da ƴan wasu ƙasashe a Asiya.
Abubuwa da dama sun jawo faɗuwar daular abbasiyawa, amma abu mai muhimmanci shi ne tawayen Faɗimiyya da tawayen Zanj da Qarmatiya, tsoma bakin sojan Turkiyya da na Daylamiyyah, a ƙarshe mayaƙan mongol na ƙasar Sin (China) suka ƙara murƙushe daular a shekara ta 1258, wato aƙalla ta kai shekaru Ɗari Uku ta na mulki ko sama da haka.
Kuma duniya ta tabbatar da cewa, har yanzu musulunci bai samu ci gaban da ya samu ta ɓangaren masana kimiyya likitanci, fasaha, da ƙere-ƙere kamar loƙacin daular abbasiyawa ba, har ana wa loƙacin kirari da (Golden age).
Daga Mahmud Habibullah Taskar Nasaba.