Dan majalisar wakilai, Alhassan Ado-Doguwa, ya yi yiwa ‘yan mazabar sa barazanar cewa, ko dai su zabi jam’iyyar APC a ranar zabe ko kuma a yi maganinsu. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai na neman komawa majalisar a karo na bakwai.
Yana wakiltar mazabar Doguwa da Tudun-Wada a jihar Kano.
Jaridar Daily Nigerian ta yi ikirarin cewa ta samu wani faifan bidiyo ne a ranar Litinin da ta gabata, wanda ke nuna Doguwa na yin wannan barazana a wani gangamin siyasa a Kano.
Rahoton ya ce, Doguwa ya yi magana da harshen Hausa ne, a yayin taron, sannan kuma ya yi amfani da kalaman batanci wajen yin barazana ga masu son kada kuri’a.
“Na rantse Da Allah da ya Halicceni, ranar zabe, ku zabi APC ko mu yi maganin ku. “Ina sake cewa: a ranar zabe ko dai ku zabi APC, ko kuma mu yi maganin ku, Ku Mai maimaita Kalamai Na, a Doguwa ko dai ku zabi APC ko kuma mu yi maganin ku,” in ji shi.
A wani labarin kuma, Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Sabon Manhajan Karatu A jami’o’in Najeriya
Gwamnatin tarayya ta sanar da sabon tsarin karatun jami’o’in kasar nan, inda ta ce, ta yi hakan ne don nuna hakikanin abin da ke faruwa a karni na 21. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a wajen kaddamar da sabon tsarin karatu a Abuja.
Osibanjo ya ce, ci gaban wani bangare ne na kokarin da aka yi na ganin ilimin jami’a ya zama mafi dacewa da bukatun al’umma.
Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ne ya wakilci Farfesa Osinbajo a wajen kaddamar da sabon tsari
Ya yi bayanin cewa gabatar da Babban Manhajar Karatu da Karamin Matsayi ga ilimin jami’a zai magance matsalolin cikin gida, da cika ka’idojin kasa da kasa da kuma bunkasa guraben karatu a jami’o’in Najeriya.
Mataimakin shugaban kasan ya kuma yabawa hukumar ta NUC bisa yadda ta sassauta nau’ukan darussa irin na, Fannin noma da samar da wasu kwasa-kwasan guda uku.