Kukan Karya Tinubu keyi a wurin yakin Neman Zabe, babban kuskuren yan Nijeriya su zabesa – Atiku.
A Jiya ne Kwamitin Yakin Neman Zaben Atiku/Okowa Suka Bayyana Cewar Sabon Tsarin Amfani da Sabbin kudade na Dan Takarar Shugaban Kasa a Inuwar Jamiyyar APC Sanata Bola Ahmad Tinubu Ya Sanya Alumma Cikin Mummunan Yanayi.
Gamayyar Kungiyar Sunce Tinubu Yana Kukan Karya ne Tare da ganin Laifin Wadanda basuji ba basu gani ba Bayan Sune suka Sanya Alumma Halinda Suke Ciki.
Kakakin Yakin Neman Zaben Kola Ologbondiyan tace, Suna Bayan Alumma Wurin Kiran Tinubu Dama Jam’iyyar sa Na APC dasu Dakatar da Wannan Yunkurin nasu.
Kuma sudaina Sanya Alumma Halin Matsi da Miliyoyin Jamaa Ke ciki saboda wani boyayyen manufa nasu.
Olagbondiyan ya Bayyana Cewar Suna sane da yunkurin wasu Gwmanonin Jamiyyar APC ke Nayin Awon gaba da Biliyan 22.5 na Sabbin Nera Dubu daya a Jihar Kano Dama Jihar Lagos.
Inda Suke Zargin Kudaden Jamiyyar APC zatayi Amfani dashi ne wurin Siyen Kuri’u yayin Zaben gama gari mai Zuwa.
Kungiyar Yakin Neman Zaben Sun Matsu su Canza Kudadensu zuwa Sabbin Kudade, Saboda Alumma sun juya masu baya , sun dogara ne kawai da siyen Kuri’u Wanda ya sabawa dokar zabe na kasa.
Wani abun ban haushi shine Yadda. Tinubu ke kukan karya, tare da danganta Laifi ga wadanda basuji ba basu gani ba duk da cewa sune ke Wahalar da Alummar kasarnan.
Yakara da cewa” Kwamitin Yakin Neman Zaben Tinubu Najin Tsoron Shan Kaye daga Jamiyyar PDP a Zaben gama gari da zaa gudanar a ranar 25 ga watan fabrairun 2023.