Kungiyar Daliban Musulmi Ta Yi Kira A Dakatar Da Rubutun Batsa A Litattafan Karatu.
MSSN ta bukaci gwamnatin tarayya ta dakatar da rubutun jima’i a cikin littattafan karatu.
Kungiyan daliban musulmi ta nijeriya MSSN B-ZONE, ta bayyana damuwanta kan shigar da abubuwan jima’i cikin wasu littattafan firamare da sakandare da ake yadawa a nijeriya a halin yanzu.
Takardan mai taken harda luwadi da jima’i a littattafan firamare da sakandare na nijeriya barazana ne ga dabi’a da kai hari kan dabi’u al’adu da addini, inda aka aika takardan zuwaga ministan Ilmi Adamu Adamu.
Takardan mai dauke da sa hannun kodineta kungiyan Qassim Odedeji,da babban sakataren kungiyan Abdujalil Abdurrazak, inda kungiyan ta bayyana rashin jin dadinta kan yadda ake nuna jima’i a wasu littattafan lissafi, turanci da social science da ake amfani dasu a yawancin makarantun sakandare a nijeriya.
Munyi mamakin abubuwan dake cikin wasu littattafan lissafi, turanci, kimiyyan zamani da ake amfani dasu a yawancin makarantun nijeriya a yau.
An gurbata wannan littattafan harsun hada da abubuwan lalata dana lalata don yin lalata da yara kanana.
Da take bayarda misalai kungiyan tace, tambayan da akeyima daliban firamare a fannin lissafi itace kwaroron roba 20 + 5 _ kwaroron roba 2 daidai.
Sun kara da cewa, wasu daga cikin littattafan suna inganta zubar da ciki, LGBT al’aura da jima’i.
Munyi imanin cewa, wannan babban cin zarafi ne ga al’adun gargajiya da addinin al’umman nijeriya, musamman al’umman musulmi.
Sunyi kira ga ma’aikatan ilmi data gaggauta gudanar da bincike kan lamarin tare da tabbatar da littattafan da ake amfani dasu a makarantun nijeriya basu da abubuwan dake da illa ga tarbiyyan matasa dalibai.
Muna bukatan ma’aikatan ilmi ta gaggauta cire duk wasu littattafan da suke dauke lalata dana lalata da ake yadawa a makarantun kasan nan.
Munyi imanin cewa, yakamata tsarin ilmin nijeriya ya kiyaye dabi’u al’adu da addinai na al’umman nijeriya musamman al’umman musulmi inji shi.
Rahoto Hajiya Mariya Azare.