Kungiyar Kwallon kafa ta Manchester City Na Fuskantar Barazanar Koro Daga Firimiyar Ingila
Sanarwar Firimiyar Ingila ta tabbatar da cewa “An tuhumi Manchester City da laifin keta ka’idojin badaqala da manyan kudi da yawa bayan binciken da aka shafe na tsawon shekaru Hudu ana yi Akan Kungiyar.
Laifin Yana iya samun hukuncin Takunkumin da za a iya yankewa idan an tabbatar da su sun da Kuma hadawa da cire maki (point)ko ma kora daga gasar a Cewar rahoton.
Bayan Jin Hakan Kungiyar Ta Manchester City tayi bayani Kamar haka:
Manchester City Tace ta yi mamakin fitar da wadannan zarge-zarge na karya dokokin Firimiyar musamman ganin yadda aka yi hadin gwiwa da dimbin cikakkun bayanai da aka samar da daga Firimiyar Ingila, Kulob din yana maraba da sake duba wannan lamari da wata hukuma mai zaman kanta ta yi, don yin la’akari da cikakkiyar shaidar da ba za ta iya murmurewa ba da ke da goyon bayan matsayinta. Don haka muna sa ran za a dakatar da wannan lamarin gaba daya a Cewar Kungiyar.
Daga: Bashir Muhammad Maiwada