Kwanciyar Aure Mai Kyau Shine Sirrin Tsawon Raina, Tsohuwa Yar Shekaru 102.
Wata tsohuwa mai shekaru 102 a duniya, Joyce Jackman ta bayyanawa duniya sirrin da ke tattare da tsawon ranta
Joyce ta bayyana cewa tarayya da namiji wanda ya iya gyara shimfida da kyau shine dalilin da yasa ta kai yawan wannan shekaru a duniya
Ta tabbatar da lallai ta mori kuruciya da kyau kuma ta samu kwanciyar aure mai inganci daga bangaren sahibinta
Wata mutuniyar kasar Birtaniya mai shekaru 102 a duniya, Joyce Jackman, ta bayyana cewa sirrin tsawon ranta ya ta’allaka ne a kan samun kwanciyar aure mai kyau.
Joyce wacce ta yi bikin cikarta shekaru 102 a duniya a ranar 9 ga watan Mayu ta tabbatar da cewar sirrin tsawon ranta yana da alaka da kwanciya da namiji.
Ta kara da ma’aikatan a gidanta da ke Essex, ta ce “kwanciyar aure mai kyau da inibi mai kyau” sune hadin da suka taimaka mani wajen tsawon rai na fiye da shekaru 100.
Da take bikin zagayowar ranar haihuwar ta da iyalinta, tsohuwar shahararriyar mai girkin ta so ace ranar ba zai zo karshe ba.
Cike da farin ciki, Joyce ta nuna mamakinta cewa za ta iya kaiwa irin wannan shekaru na tsufa.
Ta ce na ji dadin wannan rana. Na kasa yarda shekaruna 102.
“Shakka babu duk alawar da nake ci ne suka taimaka.”
Lokacin da take matashiya, Jackman ta yi aiki a shagon siyar da alawa kafin ta fara aiki da kamfanin Royal Air Force a matsayin mai dafa abinci lokacin yakin duniya na biyu.
Ta auri sahibinta na kuruciya, Terence Jackman, a 1945 lokacin da yakin ya zo karshe, sannan sun ci gaba da rayuwa cikin farin ciki.
Koda dai bata taba haihuwa ba, Jackman na son kula da yaran makwabtanta, tana mai tuna yadda take girke-girke da mahaifiyarta da fita da abokanta.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim