Rabi’u Musa Kwankwaso ya isa kasar Amurka, zai tattauna a kan abin da ya shafi takarar 2023.
‘Dan takaran shugaban kasar zai yi zama da wasu daga cikin manyan jami’an gwamnatin Amurka.
Kwankwaso mai takarar shugaban kasa a NNPP ya sanar da cewa za ayi taron a Washington DC.
Rabiu Musa Kwankwaso ya yiamfani da shafinsa na Twitter, ya shaidawa Duniya cewa jirginsa ya sauka kasar Amurka lafiya lau.
Sanata Rabiu Kwankwaso wanda yake harin kujerar shugabancin Najeriya a zaben 2023 yace zai yi zama da manyan gwamnatin kasar Amurka.
Bisa dukkan alamu a wajen taro da za ayi, ana sa ran Kwankwaso zai tattauna a kan abin da ya shafi manufofinsa da takarar 2023 da jami’an.
Kafin Kwankwaso, ‘yan takaran jam’iyyun hamayya irinsu Atiku Abubakar da Peter Obi sun je Amurka domin su shiryawa shiga takaran badi.
Na isa kasar Amurka, inda zan tattauna da wasu manyan jami’an gwamnatin kasar Amurka a birnin Washington DC.
Wani hadimin tsohon Ministan ya tabbatar da cewa tawagarsu ta isa Amurka a ranar Alhamis, amma bai yi bayanin yadda zaman zai kasance ba.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim.