Kyaftin Marquinhos Ya Karawa PSG tsawon Kwantiragi zuwa 2028
Daga karshe dai Paris Saint-Germain ta sanar da sabuwar yarjejeniya da Mai riqe da kyaftin din kungiyar Marquinhos na tsawon kwantiragi mai aiki har zuwa watan Yuni na shekera ta 2028.
Hukumar Ta PSG da Dan Wasan Marquinhos duk sun yi watsi da Tayin da duk wata dabara daga kungiyoyin Premier a kakar Wasa ta bara duk don ganin sun dau Dan wasa.
Shugaban Kungiyar Nasser Al Khelaifi Ya Bayyana Cewa “Marquinhos ya kasance yana gwagwarmaya da rigar PSG, yace ya tuna da lokacin da ya shiga kulob din yana dan shekaru Goma Sha Tara 19, Tun daga rana ta farko, ya nuna kwazo matuka da son nasarar Kungiyar”.
Daga: Bashir Muhammad Maiwada