Maɗigo Ba laifi bane Paparoma – Paparoma Francis ya bayyana dab da mutuwarsa.
Shugaban cocin Katolika, Fafaroma Francis, ya soki dokokin da suka haramta luwaɗi da maɗigo a matsayin “rashin adalci,” yana mai cewa Allah yana ƙaunar dukan ƴaƴansa kamar yadda suke.
Ya bayyana matsayinsa ne yayin wata tattaunawa ta musamman da kamfanin dillancin labarai na Associated Press ranar Talata.
“Kasancewar luwaɗi ba laifi ba ne,” in ji shi kuma ya yi kira ga limaman Katolika da ke goyon bayan dokokin hana luwadi da su yi maraba da mutanen LGBTQ cikin coci.
Francis ya yarda cewa limaman Katolika a wasu sassan duniya suna goyon bayan dokokin da suka haramta yin luwadi ko kuma nuna wariya ga al’ummar LGBTQ, kuma shi da kansa ya yi nuni da batun ta fuskar “zunubi.” Sai dai ya danganta irin wadannan halaye ga al’adu, kuma ya ce musamman bishop-bishop na bukatar yin wani tsari na sauyi don gane mutuncin kowa.
Rahoto: Shamsu S Abbakar Mairiga.