Mabiya Shi’a sun gudanar da taron tunawa da ranar 12 ga watan Disamba jiya Litinin a birnin tarayya Abuja.
Yau 12 ga watan Disamba, mabiya shi’a karkashin Jagorancin Sheikh Zakzaky suka yi taron tunawa da rana mai kamar ta jiya na wanda sojojin Nijeriya sukayi ruwan wuta kan ƴan uwansu a shekara ta 2015.
Ranar 12 Disamba, rana ce da dukkan wani mabiyi na Sheikh Zakzaky ke daukan sa a matsayin rana ta bakin ciki. Rana ce da sojoji suke daukan rana ce da ƴan shi’a suka tare wa hafsan sojoji hanya.
Shekaru 7 baya, a shekara ta 2015, anyi barin wuta a Zaria, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama. A rahoton bangaren sojin Nijeriya sun bayha cewa sama da mutane 350 ne suka mutu tare da binne su a kabari daya, yayin da su kuma ɓangaren ƴan shi’a na cewa sama da mutane Dubu ne ba a gani ba. Yayin da dama aka jikita su da harsashai masu rai.
Daga cikin waƴanda suka samu raunin harɓin harsashi akwai shugaban nasu na Ƴan uwa musulmi Sheikh Ibrahim Zakzaky, tare da matar sa Mallama Zina. Yayin da wasu daga cikin ƴaƴan su suka na cikin mutane Dubu da ake zargin an kashe su a shekara ta 2015 bayan wasu 3 da aka kashe su a shekara ta 2014 lokacin Jonathan ke karagar mulkin kasar.
Matar Sheikh Zakzaky, mafiya ga ƴaƴan sa 6 da aka she su, ita ce babbar bakuwa tayi jawabi a wajen taron tunawa da wannan ranar. Taron wanda ya gudana a baban Birnin Tarayya Abuja Nijeria. Malama Zina, ta isa filin taro, yayin da wuri ya dau kuwwa, da jinjina gare ta, wasu na basu ma iya zuwa wajen ba, saboda gani na hali da take ciki, yayin da tafiya ma dakyar take yi.
Daga cikin jawaban na ta, ta bayyana mahutuntar Nijeriya a matsayin waƴanda suke so su kawar da Harkar Isalmiyya saboda tonan asiri da da Harkar keyi na irin zalunci da mahukunta ke yi.
Malama Zina, ta bayya cewa, duk abinda Mahukunta zasu yi su yi, Harkar zata ci gaba da motsawa. Tace, “Mahukunta suna yin abun ne saboda duniya ne, kuma anan duniya, yayin da mu kuma muna yi duniya da lahira”. Ta kara da cewa, koda zasu shirya harsashi harshai, su kara da bom, wannan ba zai razana su ba.
Har ila yau, Malama Zina tace, ai sun aiwatar da abinda suka so aiwatarwa na kisa, sun sa mota sun take mutane, ciki harda yara da mata.
Bayan ta kammala jawaban ta, Malama Zina ɗin ta fito cikin yanayi, ta hau mota ta koma gida. Yayinda taron ya ci gaba da gudana, tare da sauraran jawabi na kai tsaye daga dakin jagora na Ƴan uwan musulmai din, Sheikh Zakzaky.
Daga cikin jawaban na Shugaban na su, ya fara jawabin sa ne tare da yiwa masu sauraro jajen abinda ya faru a wannan watar. Daga cikin kwanaki 3 da zasuyi na gudanar da wannan taron, 12, 13, 14, sunyi daidai da lokacin tunawa da shahadar Sayyada Fatima Azzahara Ƴar Manzon Allah (s).
Jagoran na ƴan Shia, yayi jawabi kan irin yadda mahukunta suka yi ƙeta na ƙona mutane tare kisa, yace ba zai ya rika maimaita wa ba, wanda idan mutum yana bukata sanin abubuwa game da wannan, zai iya bibiyar hurarraki da akayi da mutane kafin wannan lokaci.
Sheikh ya bayyana cewa, wannan kisa da akayi musu a 12 12 2015, ƙarƙashin mulkin Janar Buhari, ya goge duk wani abu da aka musu, wanda hakan ya ciki kundun tarihi nasu da ba zasu taba mantawa.
Daga karshe dai aka rufe taro da addu’a, an kuma tashi lafiya, ba tare da wani abu ya faru ba.
Rahoto: Mohammed Alborno.