Mafarkin Ƴan Nijeriya zai tabbata kamar yadda na kawo cigaba a legas- Tunubu
Mafarkin Ƴan Nijeriya zai tabbata daga lokacin da zama shugaban ƙasa- Tunubu…
Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, ya ba da tabbacin cewa zai cika alƙawuran yaƙin neman zaɓensa idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a shekara mai zuwa.
Da yake bayar da wannan tabbacin, jiya, a wajen wani gangamin jam’iyyarsa a garin Warri na jihar Delta, Tinubu ya koka da halin kuncin da jihar ta ke ciki, inda ya ƙara da cewa zai haɗa kai da ɗan takarar gwamna, Sanata Ovie Omo Agege, domin magance ƙalubalen rashin cigaba a jihar.
Da yake nuna goyon baya ga zaben Omo Agege a matsayin gwamnan jihar, ya ce kamfanin karafa na Delta ba na sayarwa ba ne, yana mai cewa zai tabbatar da ancimma burin mutane a ƙarƙashin gwamnatinsa.
“Zan cika alkawuran da aka yi muku. Mafarkinku za su cika a cewar Ɗan takarar.
“Ku je Legas ku ga tarihin cigaba da wadata. Burina Nijeriya ta zama haka.
Ya ce gwamnatinsa za ta yi aiki da Omo Agege a matsayin gwamna don samar da damammaki na ci gaba ga al’ummar jihar.
“Kun san cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Omo Agege, shi ne Gwamna na gaba. Zai yi aiki tare da ni, shugaban ƙasa na gaba don kawo cigaba. Omo Agege yana wakiltar sabon bege. Kamfanin ku na karafa ba na sayarwa ba ne, don ci gaba ne”.
Tun da farko, shugaban jam’iyyar na kasa, Alhaji Abdullahi Adamu, ya mika tutar jam’iyyar ga Omo Agege a matsayin mai rike da mukamai na jam’iyyar a Delta.
Shugaban wanda ya samu wakilcin mataimakin shugaban kasa, Cif Emma Eneukwu, ya yi kira ga jama’a da su zabi duk ‘yan takarar jam’iyyar a Delta.
Omo Agege kuma a nasa jawabin tun da farko, ya kalubalanci gwamnatin jihar Delta da ta yi lissafin kudaden da suka tara jihar daga kashi goma sha uku cikin dari na kudaden shiga da ake samu a cikin gida, yana mai jaddada cewa gwamnati ta gaza cimma burin jama’a.
Shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawal, tsohon shugaban jam’iyyar na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole, da uwargidan Tinubu, Oluremi, na daga cikin wadanda suka yi kira ga ‘yan Deltan da su zabi jam’iyyar a babban zaben.
Gwamna Hope Uzodima na jihar Imo da takwaransa na jihar Filato, Simon Lalong na daga cikin manyan baki da suka halarci bikin.
Daga Salma Ibrahim Dan-ma’azu Katsina