Magidanci da ya dauki budurwarsa sun je ‘hotel’, ya ci karo da matarsa tare da wani
Wani magidanci da ya dauki abokiyar sharholiyarsa zuwa Otal domin su ji dadinsu, ya ga abinda bai taba tsammani ba
Mutumin ya ga matarsa, wacce a tsammaninsa tana gida, ta zo Otal din tare da wani na daban
Wani mutumi da ya dauki ‘yar magajiya zuwa Otal domin sharholiyarsu kamar yadda suka saba ya ci karo da matarsa ta aure wacce ya baro a gida tare da nata saurayin.
Magidancin ya garzaya Otal din tare da budurwarsa domin holewa amma sai lamarin ya juye, sai ga matarsa da na ta abokin cin amanar.
Bayanai sun nuna mutumi ya nemi Otal mafi nisa da gidansa na aure domin ya hole da yarinyarsa amma duk da haka ya yi ido hudu da mai dakinsa a can.
Rahoton ya bayyana cewa mijin ya gama fitowa tsaf lokacin da ya yi karo da matarsa, kuma dukkansu sun ga juna babu wanda zai iya wayancewa ko ya yi fuska.
A Labarin da muka samu cewa wani mutun ya ja budurwarsa Otal mai nisa don su ji dadi, kawai sai ya yi kicibus da matarsa tare da wani suna fitowa daga wannan Otal din. Sun ga junansu.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim