Magidanci ya bankawa matarsa wuta har lahira a Ogun don ta yi jinjirin shirya masa abinci.
Yanda wani dan shekara 46 ya sama matar sa fetir kana ya kunna mata wuta a jihar Ogun.
Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta kama wani mutum mai suna Hassan Azeez mai shekaru 46 da haifuwa, bisa laifin zubawa matar sa fetur tare da banka mata wuta. An kama wanda ake zargin ne biyo bayan wani rahoto da mahaifin mamacin ya kai ofishin ‘yan sanda na Ibokun, wanda ya bayar da rahoto a ranar 22 ga watan Oktoba, 2022, cewa mijin nata ya kona diyarta mai suna Olayinka Hassan saboda wata ‘yar rashin jituwa da ta samu. daya, an garzaya da shi asibiti a Ibadan.
Da wannan rahoton, DPO reshen Ibogun, CSP Samuel Oladele ya yi gaggawar tara mutanensa suka nufi wurin. Amma kafin isa wurin, wanda ake zargin ya tsere. Tun daga wannan lokacin, jami’an ‘yan sandan suka ci gaba da bin sa har zuwa ranar 22 ga watan Janairu inda a karshe aka kama shi.
Da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin wanda ya yi ikirarin ya gudu zuwa Jamhuriyar Benin ya amsa laifin aikata laifin amma ya dora laifin a kan shaidan. A cewarsa, ya bukaci wanda aka kashen ta shirya masa abinci, amma maimakon wadda aka kashe ta shirya abincinsa, sai ta shagaltu da wanke-wanke. Ya ci gaba da cewa ya harzuka ne saboda yunwar da ta ji ya sanya shi zuba mata man fetur ya banka mata wuta.
Da aka tambayi matar wacece kayan sawa, sai ya furta cewa kayan sa ne. A halin da ake ciki, kwamishinan ‘yan sanda, CP Lanre Bankole, ya bayar da umarnin a mika wanda ake zargin zuwa sashen binciken kisan kai na jihar domin gudanar da bincike tare da gurfanar da shi gaban kuliya.
Rahoto: Shamsu S Abbakar Mairiga.