Magidanci Ya Bijirewa Umarnin Likita Kan Jinkirta Sàduwà Da Matarsa.
Magidanci Ya Maida Martani Ga Likitin da Ya Ce Kar Ya Kusanci Matarsa Har Kwana Bakwai.
Wani mutumi ya shiga kunci bayan Likita ya shawarce shi da matarsa kar su kusanci juna na tsawon kwanaki 7 watau mako daya
Bayan kammala yi wa ma’auratan tsarin takaita iyali, Likita ya fada musu su dan yi hakuri da juna na tsawon mako guda
Sai dai mutumin bai ji dadin wannan shawara ba domin ganinsa wannan jiran bai zama wajibi ba tunda dai an yi musu tsarin iyali
Wani magidanci ya shiga yanayin damuwa sakamakon abinda Likita ya gaya masa shi da matarsa cewa su jira tsawon mako ɗaya gabanin su kusanci juna.
Bayan an musu tsarin takaita iyali shi da matarsa, kwararren likitan ya shawarci mutumin ya hakura na dan wani lokacin kafin ya kwanta da matarsa.
Sai dai ga dukkan alamun da suka bayyana karara a fuskar magidancin bai ji dadin shawarar da Likitan ya basu ba, ya faɗa wa matar cewa su shure zancen domin ba bukatar su jira.
Lokacin da suka bar wurin likita suka koma gida, matar ta tambayi sahibin nata meyasa ya bata ransa, kuma nantake ya yi fatali da shawarar likitan.
Matar ta ci gaba da rarrashinsa tana masa kalamai nasu dadi kan ya yi hakuri. Shafin @itzz_joygray ne ya wallafa bidiyon yadda ta kaya tsakanin ma’auratan.
“Mun yi tsarin iyali, Likita ya ce mu dan jira na tsawon mako daya kafin wani abu ya shiga tsakaninmu.”
Kallo bidiyon abinda ya faru a nan
Martanin wasu mutane kan bidiyon
Bayan kallon bidiyon ma’auratan, da yawan masu amfani da soshiyal midiya sun tofa albarkacin bakinsu, wasu kuma sun faɗi abinda ya faru tsakaninsu da abokan zamansu.
@Blossom ta ce: idan da zan ce wa mai gidana ya taya ni wanke-wanke, cewa zai yi sai na ba shi wani abu. Wanda bai iya hakura da wannan ba ina ga an je babban lamari.”
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim.