Magidanci Ya Dirkawa Aminiyar Matarsa Ciki.
Wata budurwa ta yanke shawarar kin rabuwa da mijin babbar kawarta bayan ta dandani zumar sa ta ji yadda ya ke
Hakan dai ya fara ne bayan babbar kawarta ta bayyana girman kayan aikin mijinta, inda ita kuma tace bari ta tabbatar da kanta
Sai dai, ta samu juna biyu kuma ta sha alwashin sai ta haiho jaririn, inda ta ke cewa ba haka ta so ba, ita ta so ne kawai su more juna da shi
A cewarta, matar auren da babbar kawarta sun kalli wani bidiyo ne wanda ya nuna girman kayan aikin mazaje.
Sai abin ya birge budurwar, inda tace abinda aka nuna a cikin bidiyon ba gaske ba ne.
Matar auren sai ta bayyana cewa ta yarda karya ne, amma akwai maza masu irin wannan, kuma mijinta yana daya daga cikin su.
Wata shida bayan aukuwar hakan, kawai sai budurwar ta samu juna biyu tare da mijin kawarta, sannan ta sha alwashin kin zubar da cikin ko rabuwa da mijin kawarta.
“Yanzu kawarta mai juna biyun ba ta son zubar da cikin ko rabuwa da mijin. Tace ba haka ta so ya faru ba, ta so ne kawai ta dandana shi kawai a wuce wajen.” A cewar Matashiyar
‘Yan soshiyal midiya sun yi tsokaci
@Olayemiariyike ta rubuta:
“Sharrin mata kenan. Abin kunya da takaici ga mata. Matar auren ita ma tana da laifi. Meyasa za ta yi magana kan kayan aikin mijinta har ta rika tallar su ga kawarta? Ai yanzu ga shi nan ta ga sakamako, ko fara mo.”
@mogdalene ta rubuta:
“Duk wani abu da ya danganci saurayina ban yin maganar a gaban kawayena, bai ma san kawaye na ba.”
@Multi__Face ya rubuta:
“Meyasa za ki rika tallar abinda mallakin ki ne ke kadai?”
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim