Magidanci ya harbe Sirikinsa har lahira a Delta.
Rahotanni sun bayyana cewa wani mutum mai suna Iduh Hausa ya harbe sirikinsa har lahira bisa zarginsa da aikata rashin imani a garin Umunede da ke karamar hukumar Ika ta Arewa maso Gabas a jihar Delta.
Rahoton ya tattaro cewa lamarin da ya faru a Ileje, Umunede, ya jefa al’ummar cikin alhini.
Wata majiya ta ce ana tada jijiyoyin wuya a tsakanin al’umma dangane da lamarin.
“Mista Iduh Hausa ya harbe surukin sa har lahira saboda kawai shi ya yi ikirarin cewa mutumin yana soyayya da wata mace.
“Ya ce surukin yana yaudarar ‘yar uwar sa,” ya kara da cewa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Bright Edafe, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kara da cewa wanda ake zargin yana hannunsu.
Ya ce: “Eh, ya tabbata; ba mu kama wanda ake zargi ba; har yanzu yana nan. Ana ci gaba da kokarin kama shi a duk inda ya boye.”