Magidanci yayi fishi ya bar Matarsa bayan da Mahaifiyar Matarsa Ta dawo gidansu da zama.
Wani magidanci ya bayar da labarin yadda ya rasa aikinsa, sannan kuma yanayin mu’amalarsa da iyalinsa ta canza saboda rashin kudu.
Bayan rasa aikin nasa, matarsa ta ci-gaba da daukar nauyin ciyar da gidan baki ɗaya saboda ta na samun kudi fiye da mijin.
Sai dai sun fara samun matsala ne tun bayan lokacin da surukarsa ta dawo gidan nasu, wanda hakan ya yi sanadin barinsa gidan.
Wani magidanci ya bayyana yadda ya bar matarsa bayan rasa aikinsa na banki da ya yi sanadiyar jefa shi cikin halin ƙarancin abin hannu.
Labarin wanda @Ekwulu ya wallafa a shafinsa na Tuwiter, mutumin ya ce dabi’iun matarsa sun sauya daga lokacin da ta fara ciyar da gidan nasu.
Bayan ya rasa aikinsa kuma ya kasa daukar dawainiyar gidan, sai matarsa ta karbi ragamar ciyar da su saboda tana samun kudade fiye da mijin na ta.
Ya ce ya yi mamaki a lokacin da ‘yan uwan matarsa su uku suka dawo gidansu da ke Lekki a jihar Legas da zama.
Bayan nan sai ita ma surukarsa ta dawo gidan nasu, hakan ya sa ya ji ya kara takura sosai ya bar gidan kowa ma ya huta.
“Matata ke biyan kudin haya, kudin makarantar yara da dai sauransu, abin ya kara munana lokacin da aka karawa matata girma. Sai kuma surukata ta dawo gidan, wata rana da yamma ta shigo dakin cin abinci ta goranta min wai abinci ne kawai nake son ci ko da yaushe.
“Na fada mata ta daina shiga cikin rayuwar aurena, anan ne har muka yi musayar yawu. In takaice muku bayani, matata ta dawo ta tarar damu, daga nan ta fara masifa kan cewa na zagi mahaifiyarta. Gari na wayewa, na hada kaya na na ƙara gaba.”
Mutumin ya ce ya bar duk wani abu da ya mallaka a gidan, daga bisani kuma ya sha fafutuka har zuwa lokacin da ya samu wani aikin mai kyau, sannan komai ya dawo daidai.
Ya ce yanzu zai iya biyan kudin makarantar ‘ya’yansa da kula da su amma ya sha alwashin ba zai sasanta da matarsa ba.
Ita ma matar ta rasa aikinta, ta yi kokarin yin sulhu da shi, amma ya ƙi yarda da hakan..
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim.