Magoya Bayan Barcelona Suna Son Messi Ya Dawo Kungiyar.
Daga Bashir Muhammad Maiwada.
Tun Kafin Leo Messi ya bar Kulob din Paris Saint-Germain kamar yadda aka Bayyana Zai Barta Idan Kakan Wasa na shekarar 2022/2023 Ya Karshe, a watan da ya gabata Kocin Kungiyar Christophe Galtier ya tabbatar da Hakan.
Hakan Ya biyo Bayan Bayyanawar da da Kocin Kungiyar Ta PSG Yayi na Jin dadin sa Na kasancewa tare da Messi inda yake fadin cewa;
“Na sami damar horar da mafi kyawun dan wasa a tarihin kwallon kafa – Inda a karshen makon da ta Gabata ya kasance wasansa na karshe PSG a Parc des Princes da Clermont.
An Dade Ana jiyowa a mabanbantar Wasanni inda magoya Bayan Tsohuwar Kungiyar Da ya taso Acikin ta Wato Barcelona Suna ihun Suna Kiran Sunan Messi dawo dawo !
Yanzu haka dai Messi Ya bar Kungiyar Ta PSG kuma Babban Kulob Dinnan Ta Saudi Arabia Wato Al Hilal Suna zawarcin sa inda suka sa masa Zunzutun Kudi da Kai ma €400m.
Shin ya Kuke Ganin Dan Wasan Messi Zai koma Barcelonan kuwa ??