Mahara Sun Yi Garkuwa Da Malamin Addinin Musulunci.
Daga Al-Asad Al-Amin Funtua
An yi garkuwa da fitaccen malamin addinin musuluncin nan Alhaji Ibrahim Oyinlade, wanda shine babban limamin unguwar Uso, dake karamar hukumar Owo ta jahar Ondo, da misalin karfe 3:00 na yammacin yau, Asabar, 17 ga watan Yuni, 2023.
Shedun gani da ido sun shaida wa manema labarai cewa malamin yana gonar sa ne a yankin Asolo da ke unguwar Uso a karamar hukumar Owo ta jahar inda ‘yan bindigar suka kai masa hari inda suka garzaya da shi wani wuri da kawo yanzu ba a sani ba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Funmilayo Odunlami ta tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a Akure babban birnin jahar
Ta ce a yanzu haka jami’an ‘yan sanda da ‘yan banga sun shiga daji domin neman wanda abin ya shafa.
A halin yanzu dai iyalan malamin sun tabbatar da cewa masu garkuwa da mutanen sun tuntube su. Sai dai, ba su sanar da su takamaiman bukatar su ba, ko kudin fansa ba, har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto.