Mai jego ta rataye kanta a Borno.
Ana fargaban wata matan aure mai ‘ya’ya tara ta rataye kanta tabar jariri mai wata hudu a jahan borno.
Gab da magariban ranan asabat ne aka tsnici gawan maijegon a rataye a cikin gida tabar jaririnta a gefe a unguwan sajeri dake gunduman Gumari a karaman hukuman Jere ta jahan Borno.
Wani ganau mai suna Baa Modu, yace mijin matan da yaransu duka basu gida a lokacin da abun ya faru.
Yaran ne suka fara dawowa suka iske gawanta a rataye a cikin gida.
Baa Modu yace, yaran ne suka fito suka sanar da jama’a abinda suka gani.
Da muka shiga mun samu babban dan ya yanke igiyan, gawan tana kwance a kasa gefenta kuma ga jaririnta mai wata hudu.
Yace, ba’a samu wata takarda dake nuna dalilin abinda ake zargin ta aikata wanda yasa ta kashe kanta ba.
Amma wani ganau kuma makusancin iyalin yace, matakin da ake zargin matan ta dauka ya wuce gona da irine saboda rashin jin dadinta kan sauya gidansu da sukayi.
Yace, danta ya bayyana cewa bataso dawowansu gidan nan ba bayan da aka tashesu a gidansu dake Bulunkutu Kasuwa.
Don ta nuna bacin ranta saita kwashe kayanta ta koma gidan iyayenta, sai jiya aka dawo da ita, babu wanda yasan abinda zai biyo baya kenan.
Kokarin wakilinmu na samun mijin matan ko jin ta bakin kakakin ‘yan sandan jahan Borno Muhammad Shatambaya kan wannan lamari dai baiyi nasara ba.
Domin kuwa har muka kammala hada wannan rahoto kakakin ‘yan sanda bai amsa kiran wayaba.
Shi kuma mijin yatafi kaiwa ‘yan sanda rahoto amma bai dawo ba kuma ba’a sameshi a waya ba.
Rahoto Hajiya Mariya Azare.