An kama wani magidanci mai shekaru 40, Kenneth Nwangwu da laifin lalata ‘yarsa mai shekaru 9 a kauyen Akama, Igbo-ukwu, karamar hukumar Aguata ta jihar Anambra.
Rundunar ‘yan sandan ta kama wanda ake zargin ne biyo bayan samun bayanan sirri da aka samu.
Wanda ake zargin, a halin yanzu yana hannun ‘yan sanda a sashin binciken manyan laifuka da bincike na jihar (CID), Awka, duk da ya musanta zargin da ake masa.
“Wannan aikin maƙiyana ne domin suna kishina. Ina ciyar da diyata ne kawai, ba wani abu ba,” inji shi.
A halin yanzu, binciken likita da aka yi wa wanda abun ya shafa ya nuna cewa akwai matsala.
An tattaro cewa wanda ake zargin ya kasance uba daya tilo bayan matar tasa ta bar su shekaru da dama da suka wuce.
Da take maida jawabi, kwamishinan mata da walwalar jama’a, Hon. Ify Obinabo, ta yi alkawarin a shirye take don ganin an shawo kan lamarin tare da samun adalci ga kananan yara.
Ta yi Allah wadai da yawan aikata abubuwan ƙazanta a jihar, tana mai ƙarfafa guiwan kowa da kowa cewa, “koyaushe ka faɗi wani abu idan ka ga wani abu.”
Obinabo ta bayar da tabbacin cewa shari’o’in da tuni aka mika su ga babbar kotun jihar za su samu saurin gudanar da shari’a domin nan ba da dadewa ba za a fara zama babban kotun da ke cin zarafin yara da jima’i da jinsi.
Rahoto Kamal Aliyu Sabongida