Majalisa ta Dauki Zafi, Ana Sauraron Dawowar Tinubu Bayan Kwana 18 a Kasar Waje
Sanatocin APC da-dama sun dage wajen harin zama Shugaban majalisar dattawa a Nijeriya
A majalisar wakilan tarayya, masu kamfe sun yin isa wajen gaje kujerar Femi Gbajabiamila
Da alama halin da aka shiga zai iya jawo Bola Tinubu da ya bar kasar, ya dawo a makon gobe
A yayin da neman shugabancin majalisar wakilai da dattawa ya kara daukar zafi, ‘yan APC sun fara daukar mataki domin gudun a samu matsala.
Kamar yadda rahoto ya fito a Punch a ranar Lahadi, zuwa farkon mako mai zuwa ake sa ran Bola Tinubu zai katse abin da yake yi a kasar waje, ya dawo.
Idan hakan ta tabbata, ranar Litinin dinnan zababben shugaban na Najeriya zai bar duk wasu abubuwan da yake yi a ketare, ya tattara ya shigo kasar.
Ana tunanin Bola Tinubu zai dawo Najeriya domin ya shawo kan al’amuran jam’iyyar APC da suka shafi takarar shugabancin ‘yan majalisar da za a rantsar.
Halin da ake ciki a yau
Zuwa yanzu APC ta na da kujeru 57 a majalisar dattawa, LP ta na takwas, NNPP da SDP su na da biyu, sai aka samu mutum daya da ya ci zabe a YPP.
Sanatocin da ke neman shugabanci sun hada da Jibrin Barau, Sani Musa, Orji Kalu, Godswill Akpabio, Osita Izunaso, Peter Ndubuze da kuma Abdul’Aziz Yari.
Jam’iyyar APC ba ta fito ta ware yankin da za su nemi kujerun shugabanni kamar yadda aka saba yi a baya ba, hakan ya bude kofa masu takarar suka yi yawa.
A gefe guda, rahoton ya ce masu hangen kujerar Femi Gbajabiamila su na bin duk hanyoyin da za su iya wajen ganin sun kai ga nasara nan da wasu kwanaki.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim