Majalisan dattijai tabama Pantami awoyi 48 don gano inda miliyan 13.9 ta bace a ma’aikatanshi.
Majalisan dattawa tabama Isah Ali Pantami wa’adin awoyi 48 domin kawo shedan yadda ma’aikanshi ta kashe biliyan 13.9, da suka karba daga ofishin akanta janar.
Majalisan dattijai ta bama ma’aikatan sadarwa da tattalin arziki digital wa’adin sa’o’i 48 da tayi lissafin naira biliyan 13.9 na tsarin Service Wide Votes daga 2017 zuwa 2021.
Wa’adin da kwamitin majalisan dattijai kan asusu gwamnati ta bama babban sakataren ma’aikatan Willian Alo, biyo bayan gazawanshi wajen gabatar da takardun shaidu kan yadda ma’aikatan ta kashe naira biliyan 13.9 a lokacin da take tantance lamarin.
Majalisan tazo ne lokacin da shugaban Methew Urhoghide (PDP Edu ta Kudu), da wasu mombobin suka tambayi sakataren didindin na ma’aikatan sadarwa cikakkun bayanai game da yadda aka kashe kudaden da aka samu daga tsarin Service Wides Votes.
Sakataren na dindindin tare da daraktan gudanarwa na ma’aikatan sun fuskanci fushin kwamnati, saboda neman karin lokaci domin tabbatar da shaidan takardun.
Daya fusata da bukatanshi, shugaban kwamitin yace, baza’a amince da irin wannan rokon nasu ba bayan shafe watanni hudu ana bincike kan yadda ma’aikatan ta kashe kudaden.
Yace, bisa ga bayanan da kwamitin ta samu daga ofishin akanta-janar na tarayya, an raba jimillan naira biliyan 13.9 bisa wannan tsaro na Service Wides Votes da aka ware don gudanar da manyan ayyuka na musamman daga shekaran 2017 zuwa 2021.
Rahoto Hajiya Mariya Azare.