Majalisar Dattawa Ta Amince Da Kudurin Kafa Wata Hukuma Da Za Ta Rinka Kula Da Shirin Inganta Rayuwar Talakawa.
Wannan shi ne kudurin da daukacin ‘yan majalisar dattawa suka amince da shi har da ma wasu masu lalura ta musamman.
Shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Ibrahim Gobir ne ya gabatar da kudurin.
Gobir ya ce makasudin kudurin shi ne samar da hukuma bisa tsarin doka domin kula da shirin nan na inganta rayuwar al’umma NSIP da a yanzu haka gwamnati ke cewa mutane sama da miliyan dari sun amfana da shi.
Gobir ya ce Shugaba Mohammadou Buhari ne ya kirkiro da shirin a shekarar 2016 domin kawar da duk wani nau’in rashin adalci a tsakanin jama’a tare da inganta rayuwar su ta hanyar kawar da talauci, samar da ayyukan yi da kafa sana’o’in dogaro da kai, da ciyar da kananan yara dalibai kyauta ba tare da ko sisin kwabon iyayensu ba, da ba iyaye basussuka mara ruwa domin tallafa wa rayuwarsu baki daya a kasar kuma an samu nasara.
Gobir ya ce Majalisar Dattawa ta amince da kudurin. Gobir ya ce ya zuwa yanzu gwamnati ta inganta rayuwar matasa miliyan daya a shirinta na N-POWER, sannan dubu 500 na can na koyon sana’o’i iri daban daban, hakazalika gidaje miliyan daya da dubu dari shida da talatin da biyu da dari hudu da tamanin (1,632,480) sun amfana da shirin Cash Transfer ( CTP) sannan gidaje dubu hudu da dari biyu da talatin da hudu ( 4,234) sun samu naira dubu dari da hamsin (#150,000). Gobir ya ce an ciyar da yara dalibai Miliyan 9.8 ya zuwa yanzu.
Amma matashi mai fafutukar yaki da cin hanci da rashawa, Idris Bilal, yana ganin shekaru bakwai da kafa wannan gwamnati da ke cewa ta azurta mutane amma har yanzu mutane na cewa ba a gani a kasa ba, gashi har gwamnatin ta fara tattara nata i nata domin barin mulki.
Shi kuwa daya daga cikin mutane masu lalura da ke Abuja Zaiyanu Sahabi, ya yaba ne da matakin da majalisa ta dauka na kafa hukumar da za ta sa ido tare da bibiyar yadda ake aiwatar da kudaden inganta rayuwar jama’a, domin dakile hanyar wawura da almundahana da ake yi da kudaden, Majalisar Dattawa ta yi wa kudurin dokar karatu na biyu.