Majalisar Wakilai da na dattawa sun amince da saka kungiya ta yan sa kai a hukumance.
Shugaba kasa Muhammadu Buhari zai Rattaba Hannu Kan Wata Muhimmiyar Doka a Dai dai Lokacin da ya Kusa Bankwana da Mulki.
An bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya rattaba hannun kan kudirin dokar kafa hukumar yan bijilanti kafin ya bar ofis.
Babban kwamandan kungiyar na jasa shine yayi wannan kiran ga shugaban kasar a birnin Abeokuta.
Babban kwamandan ya bayyana cewa; sanya hannu kan kudirin dokar kafa hukumar ba karamin tagomashi zai kawowa tsaron kasar nan ba.
Kungiyar yan sakai ta Najeriya tayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, da ya sanya hannu kan dokar kafa hukumar yan sakai kafin zuwan ranar 29 ga watan Mayu lokacin da zai bar kan karagar mulki.
A cewar kungiyar, majalisar tarayya tuni ta amince da kudirin kafa hukumar na VGN (Establishment) Bill 2022. Rahoton Punch
Babban kwamandan yan sakan, Dr Usman Jahun, shine ya bayyana hakan a birnin Abeokuta, jihar Ogun yayin tattaunawa da ƴan jarida lokacin da ya kai ziyara kan yayan kungiyar a yankin Kudu maso Yamma.
“Majalisar wakilai da majalisar dattawa duk sun amince da kudirin dokar. Abinda kawai muke jira shine sa hannun shugaban kasa.”
“Sakon mu ga shugaban kasa shine kafin ya bar karagar mulki a ranar 29 ga watan Mayu, muna rokon sa da ya rattaba hannun kan wannan kudirin dokar domin yan Najeriya su cigaba da samun zaman lafiya da tsaro a kasar.”
Jahun ya bayyana cewa amincewa da jungiyar a hukumance zai samar da ayyukan yi sannan zai sanya jami’an yan sakai su cike gibin rashin isassun jami’an tsaron da ake fama da su a kasar nan. ALFIJIR HAUSA.
“A mafi yawa daga cikin kauyukan mu, akwai gibi sosai. Sannan akwai bukatar a cike dukkanin wadannan guraben a cikin kauyukan mu.” Inji shi
“Saboda haka, muna kira ga gwamnati da ta rattaba hannun kan wannan kudirin dokar domin mu cike wannan gibin.”
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim.