Majalisar Wakilai da na Dattijai sun amince da kudirin Uba Sani Kan Tsarin Kudi.
Majalisar Wakilan Tarayyar Nageriya ta itama tabi sahun Majalisar dattijai wajen amincewa da kudrin Zababben gwamnan jihar Kaduna Kuma Sanata Mai ci a Yanzu Sanata Malam Uba sani wannan na dauke ne a cikin wani Sakon Godiya ga Majalisar wanda Sanatan ya fitar Yana cewa A yau ne Majalisar Wakilai ta amince kudrina na “Bill For Act to Soke Nigeria Deposit Insurance Corporation Act, No. 16, 2006 and Re-Enact NDIC Act 2023 and For Other related matters (SB. 1055)”.
Majalisar a zaman ta na yau ta cimma matsaya irin na majalisar dattawa kan bukatar gaggawa ta karfafa bangaren kudi da na banki ta hanyar samar da ingantattun tsare-tsare masu inganci a matakin duniya.
Kudirin na neman soke dokar Inshorar Kuɗi ta Najeriya (NDIC) Act, 2006 da kuma maye gurbinta da sabuwar dokar da ta tanadi hukumar NDIC a matsayin mai inshorar duk wasu lamunin ajiya na inshorar cibiyoyi. Har ila yau dokar, tana neman samar da ingantaccen tsarin doka wanda zai ƙarfafawa da sake mayar da Kamfanin don sauke nauyin da ya dace; Kawo ingantuwar aiki; Daidaita NDIC Zuwa matakin mafi kyawun ayyuka na duniya don ƙungiyoyin inshorar ajiya; Ƙarfafa ikon NDIC; Riƙe masu tada hankali ga gazawar banki; gaggauta magance matsalar rugujewar bankunan da suka gaza; da daidaita su a wannan Dokar Bankuna da Sauran Cibiyoyin Kuɗi na 2020.
Ina kara mika godiyata ga shugaban majalisar wakilai da masu girma ‘yan Majalisa bisa wannan nuna kishin kasa. Wannan kudiri daya ne da ke da damar sauya fasalin kudi da na banki a Najeriya. Ina kira ga mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sanya hannu a kan kudirin doka.