Martanin Kungiyar Arewa Ta CNG ga Oduwa Ta Yarbawa zalla kan barazana da Ƙaskantar da darajar Arewa.
Hadakar Kungiyoyin Arewa (CNG), ta kideme kwarai da jin bayanan razani da barazana da kungiyar OPC ta Yarbawa zalla ta fitar kan Arewacin Nigeria. Oduwa na sukar Arewa ne kan tana kaimi wajen neman hakkokin ta a wajen zababben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
CNG na cike da mamakin ganin yanda kungiyoyin Afenifere da OPC basu yi aiki don neman nasarar Tinubu ba amma tun ba a je ko ina ba suna zakewa da nunawa duniya cewa su ‘yan uwan Tinubu ne.
Wautar dukkanin kungiyoyin da sukayi wuf suka baiyana kiyayyar su ga Arewa bayan ya ci zabe, rashin kamun kai ne da baiyana kullata.
BISA NAZARI NA ALKALUMA
Muna kira ga kungiyar OPC da su farka, su dena zama cima zaune a siyasance, suyi la’akari da alkaluma daga zaben 2023 na shugaban kasa, su fahimci yanda Tinubu ya mamayi abokan hamayya, ta nan ne zasu gane yanda Arewa ta cancanci gagarumin sakamakon da take nema a saka mata da shi.
Kuri’un da Tinubu ya samu a Arewa maso yamma Mai jihohi bakwai, yafi kuri’un da ya samu a barin sa na kudu maso yamma.
A lissafe Tinubu ya samu kuri’a miliyan biyu da dubu dari biyar da dari hudu da arba’in da biyu da dari tara da casa’in da bakwai a yankin sa na Yarbawa, yawan da yake biyewa na Arewa maso yamma.
Jiha ta biyu da tafi bawa Tinubu kuria a duk Nijeriya ita ce Kano. Ta uku iya ce Katsina.
Zuwa na biyu a jihohin Arewa da yawa, yafi zama na daya a wasu jihohin.
Misali Tinubu ya zo na daya a Ekiti, inda yaci kuri’a dubu dari biyu. Amma ya ci linkin wannan kuri’ar a Kano, inda yayi na biyu.
Tinubu ya samu.
Da fatan wannan faiyataccen bayanin zai haskawa, OPC da Afenifere rashin tasirin su a siyasar yanki da kabilanci. A wannan gabar zasu fahimce irin muhimmiyar rawar da Arewa ta taka, da hakan ya bata cancantar ta nemawa kan ta kyakkyawar makoma a siyasance.
Ba mai inkarin Tinubu ba zai kalli gudummawar Arewa ba, ta hanyar hana ta guraben da ta cancanta. Ba kuma mai hana Arewa morar ‘yancin ta na da ribatar damanmakin ta don ingantawa mutanen ta makoma.
A wannan gabar muke tabbatar da cewa ba wanda ya isa ya hana Abdul’Aziz Yari, Abbas, Betara, Gadgi, Wase, da Jaji amfani da yancin su, na neman mukamin da suke ganin zasu hidimtawa al’umma a kai.
Yan takara daga ko ina a kasar nan suna da ‘yanci su nemi mukamin da suke so, inda ‘yan majalisa suke da ‘yancin zabar wanda suke ganin ya fi cancanta.
Idan OPC na bukatar lissafin gwari-gwari kan salon yin zabe don gwamnati ta hidimtawa al’umma. Sabanin tarbiya da gurbataccen tunanin OPC na son kai da nuna wariya.
ZUWA GA SABON SHUGABAN KASA
Kamar yanda ka sani Arewa zata ci gaba da baka dukkanin goyon bayan da ka cancanta.
Muna fatan gwamnatin ka zata maida maida hankali wajen gina kasa, mai cike da hadin kai da adalci da gaskiya. Yan OPC su faminci cewa ‘yan Arewa masu neman mukamai a majalisa ba makiyan su bane.
Da yawan su, mutane be da suka zabe shi, don sun yarda da nagartar sa cewa zai kawo cigaba. Da yarda da ra’ayin sa na cewa shugabanni sune suka cancanta su bautawa al’umma ta yin amfani da ma’adanai da alkinta dukiyar kasa.
ZUWA GA OPC
Ku sani Arewa ba ta shakkar duk wasu tsageranci da kalaman barazana da kuke a kan kwanan nan. Kada kuyi kuskuren kallon kawaicin mu a matsayin gazawa. Zamu cigaba da aiki haikan don kare mutuncin yankin mu da al’ummar mu ta hanyar da ta dace da kima da mutuncin duk wani dan kasa.
Ba zamu yarda da dukkanin wani yunkuri na kaskantar da yan Arewa ba ta kowace siga.
KARKAREWA
Muna sane da yanda wasu yan siyasa a kasar nan, suka kwashe tsawon rayuwar su wajen suka da ganin baiken Arewa, wadanda suke saka su wadannan mummunan aikin suna biyan su ta hanyar ba su mukamai.
Arewa zata cigaba da kare mutuncin ta, da maida martani ga dukkanin wanda zai kawo mata raini.
Abdul’Aziz Suleiman
Kakakin CNG