Masoya Sun a Amurka sun gane su ‘yan uwa ne, na jini, bayan Shekaru 17 da aure da yara 3.
Wasu masoya a ƙasar Amurka, Celina da Joseph Quinones, sun gane cewa, su ‘yan uwana ne na jini, Bayan shafe shekaru 17 da yin aure tare da yara 3.
Masoyan sun bayyana abunda suka gane, cewar, su ‘yan uwane na jini bayan sunyo gwajin iyali na DNA.
Celina da Joseph Quinones, sun kasance tare tsawon shekaru 17, kuma sunyi aure sama da shekaru 10, Lokacin da tayi tunanin tin gwajin iyali na DNA.
A lokacin da akayi sai ta gane cewa, Joseph Dan uwan tane (Cousin), Kamar yadda ta saka a shafin ta na tiktok aka karkashin kular @realestatemommas, ta bayyana labarin.
Cewar, masoya sun gano cewa, ashe sun wuce matsayin mata da miji, Ta rubuta cewa, na aure mijina 2006, batare da tunanin komi akan ba, kuma muna da yara 3, Daga baya kuma mungane mu ‘yan uwane na jini.
Celina ta bada shawara ga masoya da su benciki kansu, Wannan lamari dai yaja hankulan jama’a inda ya samu duba ga mutane sama da milyon hudu, tare da mutane da dama da suke posting akan lamarin.
Mutane na magana ne akan yadda wadannan masoya zasu cigaba da rayuwa tare, Wasu kuma na basu shawarar rabuwa da junansu.
Ta bayyana cewa, ita tafara gano cewar, mijin nata dan uwan tane na jini,Sannan ta kara da cewa, soyayyarsu tayi girma da ba a tunani dan haka ta dakatar da sharhin da wasu keyi cewar, su rabu.
Ta rubuta cewa, muna da yara 3, kuma nayi gwajina na DNA a 2016, kuma tabbas ya dinga bani mamaki saboda a lokacin ni kamar karamar yarinya nake.
‘Yan uwa ne na jini, ko mun cancanta mu kasance tare, wannan shine abunda ya karya mun gwiwa a wancan lokacin, Bazan canja shiba saboda wannan kalmar,“miji da mata” sannan kuma zamu kasance tare har abada.
Tabbas akwai dalilin dayasa zaka ga wasu masoyan sun yi kama da junansu. Tabbas na fahimci hakan. Inda Ta kara da cewa, Yara na da mijina sune komi nawa.
Daga Rafi’atu Mustapha Katsina