Mata Ta Nemi Saki Vayan Wata Biyu Da Wure.
Wata matar aure mai suna Salamatu Suleiman, ta shigar da karar auren wata biyu bayan aurenta, saboda matsalar lafiyar mijinta.
Mai shigar da karar ta shaida wa kotun cewa ta lura cewa mijinta yana da ruwan maniyi.
Ta roki kotu da ta raba auren, inda ta ce ta gaji da auren.
Wanda ake kara ya yarda cewa yana da matsalar lafiya, amma ya dage cewa matar tana da kalubalen lafiya.
Sai dai ya ce har yanzu yana son matarsa kuma ya roki kotu da ta ba shi lokaci domin ya sasanta rikicin.
Alkalin kotun, AbdulQadir Umar, ya shaida wa uwargidan cewa ta kasance da hankali da kuma neman taimakon likita kan kalubalen da suke fama da ita.
Alkalin ya shawarci matar da ta ba da dama ta biyu a cikin dangantakar, inda ya nuna cewa duk aure yana da kalubale.
Kotun ta dage sauraren karar zuwa ranar 28 ga watan Agusta domin samun rahoton sasantawa ko kuma ci gaba da sauraren karar.
RAHOTO -ZUBAIDA ALI TARABA