Mata Zalla Za Su Rike Mukaman Kananan Hukumomin Neja Cewar Gwamnan Neja Mohammed Bago
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Bago, ya yi alkawarin cewa dukkan mataimakan shugabannin kananan hukumomi a jihar za su kasance mata a lokacin mulkinsa
Bago ya yi nade-nade biyar a baya-bayan nan, wadanda dukkansu maza ne, amma ya shirya nada mata biyar a gaba domin tabbatar da daidaito a gwamnatin tasa
Gwamnan ya jaddada kudirin gwamnonin jam’iyyar APC, na goyon bayan nasarar shugaba Bola Tinubu, ya kuma yi magana kan batun ‘yan fashi daji da suka addabi a jihar
Gwamnan jihar Neja, Umar Bago Mohammed, a ranar Talata ya ce dukkan mataimakan shugabannin ƙananan hukumomin za su kasance mata ne a gwamnatinsa.
Gwamnan ya kuma ce akwai nade-nade guda biyar da ya yi wadanda dukkansu maza ne, amma akwai nade-nade biyar masu zuwa da za su kasance mata, kamar yadda Vanguard ta wallafa.
Ya kuma bayar da tabbacin cewa ba za a samu banbance-banbance tsakanin maza da mata ba, domin za a rika raba mukaman siyasa daidai wa daida tsakanin maza da mata.
A rahoton jaridar Nigerian Tribune, gwamnan ya ce akwai yiwuwar a raba mukamai rabi da rabi tsakanin maza da mata a jihar.
Ya bayyana hakan ne bayan fitowa taron da kungiyar gwamnonin APC suka yi da Tinubu, domin taya shi murnar nasarar zaben shugabannin majalisar dokokin tarayya ta 10 da aka yi.
Bago ya kara da cewa burin duka gwamnonin jam’iyyar APC, shi ne tabbatar da samun nasarar gwamnatin Shugaba Tinubu.
Da yake amsa tambayoyi kan yadda zai tunkari kalubalen ‘yan fashin daji da suka addabi jihar ta Neja, Gwamna Bago ya ce akwai wuraren da suke a hannun ‘yan ta’adda saboda fadin da jihar take da shi, amma yana tattaunawa da jami’an tsaro kan yadda za a shawo kan lamarin.
Gwamnan ya musanta zargin da ake na cewa wasu kananan hukumomin jihar na karkashin ikon ‘yan fashin ne, inda ya ce:
“Ba mu da wata karamar hukuma da ke hannun ‘yan bindiga a yanzu, sai dai akwai ‘yan fashin a wasu kananan hukumomin.”
Ya alakanta ayyukan ‘yan bindiga a jihar da fadin kasa da jihar ke da shi, yana mai jaddada cewa Neja ta yi iyaka da kasashen waje, da wasu jihohin kasar da makiyaya ke shigowa ta cikinsu.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim