Mijina ya buge ni, ya kore ni zuwa titi saboda nace ina aiki, inji wata mata ta fada wa kotu.
Wata kotu mai suna grade a customary court, mapo, ibadan, jihar Oyo, ta yanke hukunci a kan ƙarar saki da wata mata, ramotu adetipe, ta gabatar a gabanta, akan mijinta, muyideen adetipe, a kan rikicin cikin gida, wanda ya haifar da cin zarafi.
Ramotu ta roƙi kotun da ta ba ta umarni na har abada da ya hana wanda ake kara musgunawa, barazana da kuma kutse a rayuwarta ta sirri.
Ta kuma yi addu’ar Allah ya sa muyideen ya zama cikakken alhakin kula da ‘ya’yansu.
Sedai wanda ake ƙara bai halarci zaman kotun ba duk da cewa an gabatar da shi a gaban kotu.
Ramotu a baya ta shaida wa kotun cewa, “ta haɗu da mijinta ne tun ina daliba. a lokacin yana zaune a unguwar kakata.
“Sun yi soyayya kuma suka yanke shawarar yin aure yayin da dangantakarmu tayi karfi sosai, Mijin ya yi auren al’ada kuma ya biya mata kuɗin amarya, tare da duk abinda ake nema.”
“An horar da matar yin aiki tuƙuru kuma ta yi amfani da basirarta don inganta kainta, amma mijin bai yarda da waɗannan ba.
Muyideen yana bata tallafi a matsayin alawus na kula da gida, siadai abunda yake ɓata rai baya isan su da kuma biyan wasu buƙatun da ake buƙata.
“Matar sai ta fito da wani tsari, kuma ta fara gudanar da wasu harkokin kasuwanci a lokacin da yake wurin aiki.
“Na jawo fushin muyideen ranar da ya sami labarin ayyukan matarsa kuma ya buge ta, bisani ta fice daga gidan zuwa gidansu.
“A hankali wannan yaci gaba da faruwa a gidanmu, a duk lokacin da muka sami rashin fahimta sai bugeni. Kuma tace ‘Yan uwansa suke haddasa matsala. kullum suna kawo fitina a gidanmu kuma su haifar da sabani tsakanin ni da mijina.
“Ba su taɓa jin daɗin ƙoƙarina na ba, koyaushe suna yin Allah wadai da girkina, Duk lokacin nakai karan shi, sai suna goyon bayan shi.
Ya buge ni a lokacin da nake da ciki na biyu kuma na kusa rasa cikin na wata biyar bayan na fita aiki, Na fita daga gidansa tare da yaran mu bayan wannan kuma na yi hayar gida.”
Da take yanke hukunci, shugabar kotun, Mrs s.m akintayo, ta bayyana cewa babu wani auren da za a raba. ta kara da cewa shaidar da mai gabatar da kara ta bayar dangane da cin zarafi da rashin tausayi ba ta kalubalanci wanda ake kara ba a lokacin da aka ba shi damar yi masa tambayoyi tun da ya kasa zuwa kotu.
Ta kuma umurci wanda ake kara da ya rika biyan N30,000 duk wata domin kula da ‘ya’yansu. dukkansu an wajabta musu alhakin kula da karatunsu.
Rahoto Kamal Aliyu Sabongida.