“Matar aure mai suna Saudatu, mai Shekaru 36 a duniya, haifaffiyar tudun Wadan Zariya. ta saki mijinta mai suna Aminu tare da aje masa takardan sakinsa a gaban magabantansa.”
“Lamarin ya samo asaline sakamakon rashin sauke nauyin haƙƙoƙin aure waɗanda suka rataya a mijin, ganin yadda ita ke bin danginta suna taimaka mata kuma shi mijin nata ba naƙasashe ba bare ace ba zai iya fita neman na kansa ba, kamar yadda Saudatu ta bayyana hakan.”
Bugu da ƙari matar tana zargin mijin nata da bibiyan maza kamar yadda matar ta shiada hakan a gaban magabatansa.”
“Saudatu ta share shekaru masu yawa tana auran Aminu, inda lamarin ya cutura bayan shi mijin yace bai saku ba kuma yana son matarsa.”
“A halin yanzu dai ƳaƳansu 9 a tsakani, inda magabatan mijin nata suka yi mata gyara da cewa ba sakinsa za tayi ba jingine auren ake yi, amma hakan da ta yi na furucin saki ya saɓawa addinin musulunci.”
“A ƙarshe dai Saudatu ta aminta da jingine auran, tare da amsan kuskurenta bayan furucin da tayi a baya na cewa ta saki mijin nata, amma kuma ta ce bazata fita daga gidansa ba tana nan daram zaman ƳaƳanta zata yi inda shi kuma mijin nata bai musanta hakanba.”
“A ta ɓangaren mijin kuma an jiyo cewa mijin nata kamar yadda shima ya furta haka! zargin da matarsa take masa na bibiyar maza ƙaryane kawai ta yi amfani da wannan damarne domin ta cimma burinta.”
“A halin yanzu dai tuni mata tace ita ta jingine aurenta da Aminu har sai ya gyara munanan halayyarsa sannan zata cigaba gaba da basa haƙƙinsa a matsayinta Na matarsa.”