Wata mata mai suna ada ta bayyana cewa ta samu ciki kuma ta haihu amma a saninta babu namijin daya taba saduwa da ita. Wonder 9ja.com ta rawaito.
Yayin tattaunawa da matan a STEP TV, matan tace shekaru hudu kenan datasan cewa babu namijin da ya taba ko rike hannunta balle sukai ga saduwa.
A cewanta, koda taji ciwon cikin tayi tunanin FIBROID ne ba juna biyu ba, yayinda ta isa asibiti tace anbukaci yimata aiki don cire abinda ke cikinta.
Ta kara da cewa tayi iya kokarinta na turo Fibroid saboda tsoron kada ayi mata aiki amma ga mamakinta sai santalelen jariri ya fito.
Matan wacce ke sayarda ruwa a bakin titi ta shaidawa manema labarai cewa bata da kudin kulawa da jaririn a halin yanzu.
Saidai akwai matan wani fasto data ke kulawa da yaron tun lokacin da aka haifeshi harzuwa yanzu tana iyakan kokarinta.
Rahoto Hajiya Mariya Azare.