Matar da tayi Yunkurin sace jariri ta mutu a Asibiti bayan matasa sun gallaba mata azaba a Legas
Wata mata da ake zargi mai suna Toyin, wadda wasu fusatattun mutane suka azabtar a lokacin da ake zarginta da yunkurin sace jariri dan wata takwas a unguwar Ebute-Metta da ke jihar Legas, ta mutu a asibiti. .
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar wa da wakilin Punch faruwar lamarin a ranar Alhamis.
Ya ce Toyin na kwance a asibitin gwamnatin tarayya da ke Ebute-Meta, saboda ta kone sosai daga fusatattun ’yan iska da suka kama ta tana aikata wannan haramtacciyar hanya.
“Matar ta mutu a asibiti,” in ji Hundeyin.
PUNCH ta ruwaito cewa wanda ake zargin ta shiga gidan wani dan uwan mahaifiyar jaririn ne domin neman mijinta, Akeem.
Bayan an sanar da ita cewa mijinta ba ya cikin harabar kuma daga baya aka ba ta shawarar ya bar gidan, daga busani Toyin ta bar ginin.
Da ta fahimci cewa baban yaran ya tafi, sai ta koma cikin ginin, aka ce ta yi yunkurin sace jariri.
Wata yarinya ‘yar shekara 11 da ke tare da yaran ta hana ta tare da daga murya, lamarin da ya sa mazauna unguwar suka kama Toyin.
An kai wanda ake zargin a karkashin gadar da ke unguwar Ijora, inda wasu fusatattun mazauna yankin suka yi yunkurin kashe ta amma daga baya ‘yan sanda suka shiga tsakani suka tafi da ita.
Hundeyin ya ce Toyin ya samu munanan konewa a lokacin harin kuma tana kwance a asibiti.
Rahoto: Kamal Aliyu Sabongida