Matar Wani Attajirin Mai Kudi Ta Siyar Da Wayar Ta Domin Ceto Ran Mahaifiyarta
Wata mata ta ce ta ji bakin cikin yadda attajirin mijinta ya ki taimakawa mahaifyarta don yi mata tiyata
Ta ce mjin nata yana da ‘yan mata da yawa da yake taimaka musu da kudade da dama amma ita ko kwabo ba ya bata
Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu yayin da wasu suka tausaya mata, wasu kuma ke cewa ta nemi hakkinta a kotu
Wata mata ta bayyana yadda ta siyar da wayarta don samun kudin da za a yi wa mahaifiyarta tiyata bayan mijinta ya ki taimaka mata.
Ta ce ta ji bakin ciki ganin yadda mijinta ke da makudan kudade amma sai dai ya kashewa ‘yan waje ko kuma ‘yan matansa na layi.
Matar wadda batason bayyana sunanta ta yada a wata kafar sadarwa ta Instagram, @couplestherapies don neman shawara.
Ta ce mijinta ya taba kashe naira miliyan 2.1 don taimakawa yayin bikin binne mijin wata mata, ya kuma siya mata wayar hannu da mota wadda ita kuma ko kudin bukatunta ba ya bata.
Ta kara da cewa ta roki mijinta ya taimaka mata da N380,000 don rashin lafiyar mahaifiyarta amma yaki, yayin da kuma ya kashewa budurwarsa N250,000 saboda bikin ranar haihuwarta.
A cewarta na shiga yanayin bakin ciki. Na siyar da wayata don samun kudin yin tiyata ga mahaifiyata, amma na fadawa mijina cewa an sace wayar ne. Da naga zai yi bincike sai na fada masa gaskiya, yayin da ya ce zai kore ni a gida idan ban dawo da wayar ba.”
Ta ce ta kai karar sa zuwa wurin Fastonsu amma ya ki zuwa, inda wata mata a majami’ar ta ba ta kudin tiyatar da kuma shawartarta akan ta nemo hanyar da za taraba zama da shi.
Ta kara da cewa da karbo wayar na bawa mijina, kuma bazan sake amfani da wayar ba har sai na siya da kudi na. Ina tsammanin na auri makiyi na, mutanen wannan gida kuba ni shawara ina son barin gidansa amma bana so mambobin majami’ar mu suce ban dauki shawararsu ba.”
Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu, yayin da wasu ke tausaya mata, wasu kuma cewa suke ta nemi hakkinta a kotu, wasu kuma sun bata shawarar ta yi addua don neman mafita.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim