Matashi ɗan Shekara 24 da ya auri baruriya mai shekaru 61 ya koka na rashin haihuwa.
Daga Wakilinmu.
Bariya yar thekara 61, ta auri wani Matashi ɗan shekara 24 a ƙasar Amurka.”
Rahoton ya ci gaba da cewa; bayan sun shafe kusan shekara ɗaya suna soyayya, daga ƙarshe suka yanke shawarar su yi aure.”
Ya’yanta da ta haifa tsakaninta da Tsoho mijinta da ya mutu ƴan shekaru 30 zuwa 41, sun ce za su taimaka mata wajen renon jariri ko jaririya dazaran ta haifa da shi wannan Matashin.
Shi dai wannan matashin da ya auri baturiyar ɗan Asalin ƙasar Barkina faso ne, Bisani kamar yadda ALFIJIR HAUSA ta bibiya lamarin ta gano cewa; Matashin ya ƙagu da ganin baruriyan ta haifan masa jariri ko jaririya.”
Bugu da ƙari Matashin ya ce zai ci gaba da gwada kwazonsa don ganin ya Tabbatar matarsa baruriyan ta samu ciki.