“Wani matashi, mai suna iliya haifaffen garin Zariya jihar Kaduna ya dirƙwa budurwansa ciki mai shekaru 25, hakan yana da Nasabar raba su da aka yi lokaci mai tsawo, sakamakon cewa da iyayenta suka yi su baza su ba shi ba.”
Budurwansa mai suna Sa’adiya ita kuma ta ɗaura hannu a bisa ka ataf shi take so, saboda sun daɗe suna soyayya, kuma soyayyar nasu a fili yake kowa ya sani, kama har sauran dangi da abokanan Arziƙi.
Wakilinmu ya tabbatar mana faruwar lamarin, wanda ake zargi ɗin da dirƙawa budurwan ciki a tashin farko ya nesanta kansa da wannan al’amari, sai dai an iya jiyo ta bakin Sa’adiya inda ta gabatarwa iyayenta cewa shine ya driƙa mata ciki rugum, biyo bayan haɗuwa da suke yi a bayan fage.”
“A halin yanzu dai, bayan zama tare da tattaunawa da aka yi tsakanin dangi, an samu matsayar da a zubar da cikin, inda masana kiwon lafiya suka tabbatar cewa cikin har ya fara ƙwari.