Matashi daga Afirka ya yi tattaki zuwa kasar mawakiya Rihanna don Neman aurenta.
Wani mutum da daga Afrika wanda ya yi tattaki zuwa Los Angeles daga South Carolina kuma ya bayyana a gidan Pop star Rihanna na Beverly Hills don neman mawakiyar, ‘yan sandan Los Angeles sun tsare shi ranar Alhamis.
Kamar yadda DailyMail ta ruwaito a ranar Alhamis, mutumin ya isa gidan mawakiyar inda ya sanar da jami’an tsaronta ya yi tattakine na musamman daga Afrika Domin zuwa Neman aurta.”
Tawagar Rihana da jami’an tsaronta ne suka sanar da ‘yan sandan, inda suka iso, suka daure mutumin a hannu, suka saka shi a cikin mota, sannan suka tattauna da shi sosai kan manufarsa.