Matashi Ya Ciji Yatsan Wani Mutum Ɗan Shekara 50 Saboda Kallon Mahaifiyarsa.
Wani matashi a jihar Adamawa ya fusata ya cije kan yatsan wani da ya zarga da kama ƙurawa mahaifiyarsa idanu.
Aliyu Adamu, mai shekaru 18, ya amsa laifin cin zarafin da ya yi wa Yautai Adamu mai shekaru 50 bisa zarginsa da kallon mahaifiyarsa wacce keda shekaru 40 a duniya.
Yaron da mahaifiyarsa duk ‘yan garin Mairawani ne a garin Jambutu a ƙaramar hukumar mulkin Yola ta Arewa.
An bayyana cewa wanda ake zargin yana kan hanyarsa ta fitowa daga gidansa ne a ranar Lahadi 4 ga watan Disamba, inda ya ci karo da Aliyu Adamu da mahaifiyarsa.
Kamar yadda rahoton DailyPost ya ruwaito, lokacin da Aliyu ya juyo ya ga Yautai ya zubawa mahaifiyarsa ido, ya sai ya ƙalubalanci matashin mai matsakaicin shekaru, kuma ba tare da jiran amsa ba, sai ya yi masa ruwan zagi, lamarin da ya sa aka rika yin musabaha har ya kai ga cizon yawutai a hannunshi na dama.
Daga nan ne aka gurfanar da Adamu a gaban kotun yankin Jimeta II da ke Yola ta Arewa a kan tuhume-tuhume uku da suka haɗa da cin zarafi da kuma haddasa mummunar ɓarna.
A cewar ɗan sanda mai shigar da ƙara, Kofur Ismail Mohammed, yace laifukan da wanda ake ƙara ya amsa laifinsa, ya ci karo da sashe na 240, 241 da 217 na kundin laifuffuka.
Bayan da wanda ake tuhuma ya amsa laifinsa a kotun da Hon Muhammad Lamurde ya jagoranta, an tsare shi a gidan yari tare da ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 3 ga watan Junairu, 2023 domin yi masa shari’a.
RAHOTO:- Comrd Yusha’u Garba Shanga.